in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Wang Yi: "Zirin daya da hanya daya" sabuwar hanya ce ta samun bunkasuwa da wadatar kasashen duniya baki daya
2018-05-18 11:18:39 cri
Ministan harkokin wajen kasar Sin Mista Wang Yi, ya gana da takwaransa na kasar Faransa Jean-Yves Le Drian, a jiya, tare kuma da zantawa da manema labarai.

Yayin taron manema labaran, Mista Wang ya bayyana cewa, shawarar "Zirin daya da hanya daya" ta samo asili ne daga kasar Sin, amma zarafi da ci gaban da ta kawo na amfanawa duniya baki daya. Wang Yi ya ce, shekaru biyar bayan gabatar da wannan shawara, yawan kudin da ya shafi ciniki tsakanin Sin da kasashen da suka amince da shawarar, ya kai dala biliyan 4000, kana kuma yawan jarin da aka zuba ya kai dala biliyan 60. Ban da wannan kuma, Sin ta bude hanyar jiragen sama kai tsaye zuwa wadannan kasashe 43, tare da zirga-zirgar jiragen kasa sau 7500 tsakaninta da kasashen Turai, har ma ta kafa yankin hadin gwiwa ta ciniki a kasashen waje guda 75, matakin da ya samar da guraben aikin yi da ya zarce dubu 200. Duk wadanan abubuwan, sun shaida cewa, shawarar "Zirin daya da hanya daya" ta dace da bunkasuwar tattalin arzikin duniya ta bai daya, tare da kawowa jama'ar da shawara ta shafa, dimbin alfani. A cewarsa, wannan shawara dai, ta fidda wata sabuwar hanyar raya kasashen duniya mai wadata, dake kawo makoma mai haske bisa yanayin da ake ciki a halin yanzu na rashin tabbas. (Amina Xu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China