A lokacin da yake Windhoek, babban birnin kasar, Li ya gana da shugaban kasar Hage Geingob da tsohon shugaban kasar Sam Nujoma. Haka kuma Li ya tattauna da Katjavivi da shugabar majalisar zartarwar kasar Magreth Mensah-Williams.
Mr Li ya ce ziyarar da Geingob ya kawo wa kasar Sin a watan Maris din da ya gabata ya bude wani sabon babi a dangatakar dake tsakanin kasashen Sin da Namibia, abin da ya sa shugabannin kasashen biyu yanke shawarar daga matsayin alakar kasashen zuwa manyan tsare-tsare.
Ya kuma bayyana cewa, kasar Sin tana fatan sassan biyu za su hada kai wajen karfafa tattaunawa bisa manufa da daidaita shiryen-shiryen ci gaba ta yadda zai dace da shawarar ziri daya da hanya daya, da dandalin hadin gwiwar Sin da Afirka(FOCAC), da bunkasa hadin gwiwa a fannin gina ababan more rayuwa da raya masana'antu ta yadda za su amfanawa al'ummon kasashen biyu. (Ibrahim)