Shugaban zaunannen kwamitin majalisar wakilan jama'ar kasar Sin NPC Li Zhanshu ya kai ziyarar karfafa dangantaka a kasar Mozambique tsakanin ranakun Asabar zuwa Talata, da nufin kyautata mu'amala tsakanin kasashen biyu.
Li, ya gana da shugaban kasar Mozambique Filipe Nyusi a Maputo, babban birnin kasar, kana ya zanta da shugabar majalisar dokokin kasar Veronica Macamo.
A lokacin ganawar tasu da shugaba Nyusi, Li ya ce, kasar Sin ta taimakawa kasar Mozambique a kokarinta na neman 'yancin kai da kuma samun dawwamammen ci gaba, kuma za ta ci gaba da taimakawa Mozambique din wajen samun ci gaba cikin sauri.
A nasa bangaren, shugaba Nyusi ya ce, kasar Mozambique a shirye take ta shiga shirin raya shawarar ziri daya da hanya daya, da kuma zurfafa mu'amala da kasar Sin a fannonin aikin gona, makamashi, masana'antu, yawon bude ido da gina kayayyakin more rayuwa, da nufin daga martabar dangantakar dake tsakanin kasashe biyu zuwa matsayin koli.
A lokacin tattaunawarsa da shugabar majalisar dokokin kasar Macamo, Li ya ce, NPC a shirye take ta kulla kyakkyawar alakar abokantaka da majalisar dokokin kasar, da kuma yin musayar kwarewa a matakai daban daban da takwararta ta kasar Mozambique, da kuma tabbatar da ganin an aiwatar da dukkan yarjejeniyoyin hadin gwiwar da aka kulla tsakanin bangarorin biyu.(Ahmad Fagam)