Dan wasan dan kasar Masar, shi ne dan wasan Afirka na farko da ya ci kwallaye sama da 30 a kaka daya. Shi ne kuma na farko da ya lashe kyautar dan wasa mafi hazaka ta wata-wata har karo 3 a jere a dai kakar ta bana.
Salah, wanda ya koma Liverpool a kakar bara, ya kuma fara buga gasar firimiya bayan barin sa gasar a kakar shekarar 2013 zuwa 2014 lokacin da ya yi wasa a Chelsea, ya bayyana farin cikin sa da nasarorin da yake samu a yanzu haka.
Ya ce "Ba wannan ne karo na farko da na samu nasara a wannan fage ba, don haka neman nasara na cikin raina a wannan gasa ta firimiya."
Sallah ya cimma nasarar sa a wannan karo ne, bayan kwararru sun kada kuri'u na tabbatar da kasancewar sa zakaran gwajin dafi a gasar firimiya.
Ya shige gaban sauran 'yan takarar wannan karramawa, wadanda suka hada da Kevin De Bruyne, da David De Gea, da Harry Kane, da Raheem Sterling da kuma James Tarkowski.
Karramawar da Sallah ya samu ta zamo kari kan wadda hukumar PFA, da kungiyar marubuta wasanni suka yi masa, duka dai a kakar ta bana.(Saminu Alhassan)