Neymar, wanda Barcelona ta sayarwa PSG shi kan kudi har Euro miliyan 222 a watan Agustar bara, bai taba boye burin sa na zama zakaran kwallon kafa na duniya ba.
Amma a ra'ayin Rivaldo, wanda shi ma ya taba lashe kyautar dan kwallon kafa mafi hazaka ta Ballon d'Or a shekarar 1999, sai Neymar din ya amince ya koma Real Madrid kafin ya cimma nasarar da yake fata.
Ya ce "A gani na idan ya zauna a PSG ba zai zamo dan wasa mafi hazaka ba". "dole ya bar PSG ya koma Sifaniya. In ka duba da kyau, akwai Ingila, da Sifaniya, da Italiya da Jamus akwai takara mai yawa. Zai yi wuya ya koma Barcelona. Amma ina ga yana da damar buga wasa a Real Madrid. Idan ya koma can tabbas zai iya zama dan kwallon duniya" A kalaman Rivaldo.
Neymar ya ciwa PSG kwallaye 28, ya kuma taimaka an ci wasu 16 a kakar wasa ta bana, kafin ya samu ciwo a kafa a watan Fabarairun da ya gabata.
Ana sa ran Neymar dan shekaru 26 da haihuwa zai koma taka leda nan da wata guda, amma Rivaldo ya ce dole Brazil ta shirya maye gurbin Neymar a jerin 'yan wasan da za su wakilci kasar, duba da cewa ba lallai ba ne matashin dan wasan ya murmure yadda ya kamata nan da ranar 14 ga watan Yuni, lokacin da za a fara buga gasar cin kofin duniya a kasar Rasha.(Saminu Alhassan)