in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Namibia ta rasa damar buga gasar kwallon kafa ta 'yan kasa da shekaru 20 ta nahiyar Afirka
2018-04-25 13:40:55 cri
Kungiyar kwallon kafar kasar Namibia ta matasa 'yan kasa da shekaru 20, ta gaza samun gurbin shiga gasar cin kofin duniya na hukumar FIFA da za a gudanar a shekarar badi, bayan da ta tashi kunnen doki 1 da 1 da Botswana a wasan ranar Lahadi a filin wasa na birnin Windhoek.

Da wannan sakamako, yanzu Botswana ta samu damar buga wasannin zagaye na 2 na neman gurbin da ake bugawa. Kuma janhuriyar Nijar ce za ta karbi bakuncin wasan karshe na wannan mataki. Kungiyoyi 4 da suka kai ga wasan kusa da na kusan karshe ne za su samu gurbin buga gasar cin kofin duniya na hukumar ta FIFA na 2019 ajin matasa 'yan kasa da shekaru 20.(Saminu Alhassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China