180426-An-yi-Allah-wadai-da-tashin-hankalin-wasan-Afirka-ta-Kudu-zainab.m4a
|
Wasu 'yan kallo ne dai suka afka cikin filin wasan a karshen mako, bayan da aka doke kungiyar su da ci 2 da nema a gasar cin kofin Nedbank, inda nan take suka haifar da hargitsi wanda ya lahanta wasu 'yan kallo.
Da yake tsokaci game da aukuwar lamarin, ministan wasanni na kasar Tokozile Xasa, ya ce dole ne a bayyana hakikanin abun da ya auku da almurun ranar Asabar, bayan wasan da aka doke kungiyar night Kaizer.
Rahotanni sun bayyana cewa, magoya bayan kungiyar sun kaiwa masu gadin filin wasan hari, sun kuma lalata wasu kayayyakin wasa dake cikin filin, baya ga wadanda aka raunata su 18. Kawo yanzu dai an kama mutane 2 bisa zargin su da hannu a aukuwar lamarin.
Ita ma hukumar wasanni ta Afirka ta kudu Sascoc, ta yi Allah wadai da aukuwar tashin hankalin. A cewar shugabanta Gideon Sam, ba za a taba amincewa da wannan halayya ba.
Gideon Sam ya ce, hukumar kwallon kafar kasar PSL, da shugabannin filin wasan, dole ne su yi bayani game da abun da ya faru. Ya ce tashin hankali ba zai taba warware wata matsala ba. Kaza lika ya kara da cewa, ba za su taba kyalewa magoya bayan kungiyoyin kwallon kafa suna haifar da tashin hankali ba, musamman ma duba da yadda wasan kwallon kafa ke hade kan al'umma.
Ya ce yana fatan dukkanin masu ruwa da tsaki za su hada kai da Afirka ta kudu wajen tabbatar da hukunta wadanda suka aikata wannan laifi.(Saminu Alhassan)