Rahotanni sun bayyana cewa, kocin zai koma gida ne domin maida hankali ga horas da kungiyar kasar sa.
Ita ma dai kungiyar ta Zenit ta bayyana cewa, ta cimma matsayar kawo karshen kwantiragin ta da Mancini, bayan kammala kakar wasanni ta bana, biyowa bayan cimma matsaya da suka yi tare da shi.
Kafafen watsa labarun kasar Italiya sun bayyana cewa, dan wasan mai shekaru 53, zai karbi ragamar horas da kungiyar kasarsa ne cikin mako mai zuwa. Italiya ba ta samu gurbin buga gasar cin kofin duniya da za a fara a Rasha cikin wata mai zuwa ba, wanda hakan shi ne na farko cikin shekaru 60 a tarihin kungiyar.
Mancini ya lashe kofuna 26 a tarihi. 13 cikinn wannan adadi a matsayin sa na dan wasa, kana 13 lokacin naya mai horas da 'yan wasa, ciki hadda kofunan gasar Serie A ta kasar Italiya, lokacin yana tare da Inter Milan. Sai kuma kofin da ya dauka lokacin da yake horas da kungiyar Manchester City a gasar firimiya.(Saminu Alhassan)