in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kungiyar wasan kwallon kafa ta mata ta kasar Brazil ta dau kofi a karo na 7 na gasar Copa America
2018-04-25 13:37:24 cri
A ranar Lahadin da ta gabata, kungiyar wasan kwallon kafa ta mata ta kasar Brazil ta cimma nasarar daukar kofin Copa America, wanda ya ba ta damar samun tikitin shiga gasar cin kofin duniya na mata ta shekarar 2019 da za a gudanar a kasar Faransa, da kuma gasar wasannin Olympics ta shekarar 2020 da za a gudanar a birnin Tokyo na kasar Japan.

Kafin wasan karshe, kungiyar Chile ta doke kungiyar Argentina da ci hudu da nema, don haka kungiyar kasar Brazil ta riga ta zama zakara tun kafin ma ta buga wasan karshe tare da kungiyar Colombia.

Bisa jagorancin tsohon mai horaswa na kungiyar Corinthians Oswaldo Fumeiro, kungiyar wasan kwallon kafa ta mata ta kasar Brazil za ta yi wasan na karshe ne a ranar Lahadi, bayan da ta riga ta cimma nasara a wasannin ta 6 na wannan karo.

Kungiyar wasan kwallon kafa ta mata ta kasar Brazil ta riga ta dauki wannan kofi har sau 7 ke nan, bayan da aka fara gudanar da wasan Copa America karo na 1 a shekarar 1991. Kungiyar Argentina ita ce kungiya daya tak da ta taba cimma nasarar daukar wannan kofi sau daya tak a gasan a shekarar 2006. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China