in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mataimakin Firaministan kasar Sin ya gana da mambobin majalisun dokokin Amurka
2018-05-17 14:03:07 cri
Manzon musammam na Shugaban kasar Sin Xi Jinping, kuma mataimakin Firaministan kasar wato Liu He, ya gana a jiya Laraba, da tsohon Sakataren harkokin wajen Amurka, Henry Kissinger, da wasu 'yan majalisar dokokin kasar, dangane da dangantakar Sin da Amurka

Liu He ya isa birnin Washington ne da yammacin ranar Talata, domin tuntubar bangaren Amurka, game da harkokin tattalin arziki da cinikayya, bisa gayyatar Amurkar.

Liu He wanda kuma ke shugabantar tawagar kasar Sin mai tattauna harkokin tattalin arziki da Amurka, shi ya jagoranci mambobin tawagar da suka fito daga manyan bangarorin tattalin arziki na Gwamnatin kasar Sin, zuwa Amurka.

Yayin ganawarsa da Henry Kissinger, Liu ya bayyana cewa, ziyarar da yake yi a Amurka, na da nufin ci gaba da tuntunbar kasar game da huldar cinikayya da tattalin arziki dake tsakaninta da kasar Sin, kamar yadda shugabannin kasashen biyu suka cimma.

A ganawarsa da mambobin majalisun dokokin kasar kuwa, Li ya ce jajircewar kasashen biyu na tsayawa tsayin daka da kyakkyawar hulda, ya dace da muradun al'ummominsu da kuma na sauran kasashen duniya. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China