in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Trump: Amurka za ta janye jiki daga yarjejeniyar nukiliyar Iran
2018-05-09 08:42:44 cri

Shugaba Donald Trump na kasar Amurka ya sanar jiya Talata cewa, kasarsa za ta janye jiki daga yarjejeniyar nukiliyar kasar Iran.

A cikin jawabinsa a fadar White House, Trump ya ce, yarjejejniyar nukiliyar Iran ba ta da kyau sam. Kana kasarsa za ta sake sanya takunkumi kan Iran, wanda aka dakatar da shi bisa yarjejeniyar.

A watan Yulin shekarar 2015, Iran da kasashen Amurka, Birtaniya, Faransa, Rasha, Sin da Jamus suka daddale wata yarjejeniya kan batun nukiliyar Iran daga dukkan fannoni, inda Iran ta yi alkawarin dakatar da wasu ayyuka da aka tanada cikin shirinta na nukiliya, tare da yin amfani da makamashin nukiliya ta hanyar da ta dace, yayin da kasashen duniya suka dakatar da takunkuman da suka sanya mata. (Tasallah Yuan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China