in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Trump ya sanar da tawagar da za ta halarci bikin bude ofishin jakadancin Amurka a birnin Kudus
2018-05-08 11:07:38 cri

Shugaban kasar Amurka Donald Trump, ya sanar a yau cewa, zai tura wata tawaga ta musamman zuwa Isra'ila don halartar bikin bude ofishin jakadancin Amurka a birnin Kudus.

Wata sanarwar da fadar shugaban ta gabatar, ta ce za a gudanar da wannan biki ne a ran 14 ga wannan wata, inda mataimakin sakataren harkokin wajen kasar John Sulivan, zai jagoraci tawagar. A makon da ya gabata ne, Trump ya bayyana cewa, watakila shi zai halarci bikin.

Da farko a jiya Litinin, Sakatare Janar na kungiyar 'yantar da al'ummar Palasdinu (PLO) Saeb Erekat, ya yi kira ga kasashen duniya su kauracewa halartar bikin bude ofishin jakadancin Amurka a birnin Kudus.

Jami'in na PLO ya ce, mahalartan biki, za su nuna wata alama maras kyau, wadda za ta goyi bayan matakan sabawa dokokokin kasa da kasa da halaltattun hakkokin Palasdinawa. (Amina Xu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China