Jami'an na daga cikin ayari mai mambobi 395, wanda ya kasance ayari na 6 da aka tura kasar.
Ayarin, zai gudanar da ayyukan da suka hada da samar da tsaro da kula da wadanda suka ji rauni.
Za kuma a dora musu aikin kula da tituna da hanyoyin jirgi da kuma tsaftar muhalli da kare barkewar cututtuka.
Tun daga farkon bana ne aka fara ba jami'an horo kan dabarun yaki.(Fa'iza Mustapha)