Lamarin na zuwa ne kwana guda bayan da wasu sojojin kasar Mali 6 suka mutu a wani harin da aka kaddamar a tsakiyar kasar.
Wata sanarwar da kakakin Guterres Stephane Dujarric ya fitar, ta ruwaito shi ne yana cewa, hare-haren da aka kaiwa jami'an MDD dake aikin wanzar da zaman lafiya tamkar aikata laifukan yaki ne karkashin dokokin kasa da kasa, don haka wajibi ne a zakulo tare da hukunta wadanda suka aikata shi. (Ibrahim)