in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
MDD: An hallaka jami'an wanzar da zaman lafiya 4 a harin bom a Mali
2018-03-01 10:20:15 cri
Mai magana da yawun MDD Stephane Dujarric, ya bayyana cewa, an hallaka jami'an kiyaye zaman lafiya na MDD a Mali 4, kana an raunata wasu jami'an 4 a jiya Laraba a lokacin da motar MDDr dake dauke da jami'an ta haura kan wasu boma-bomai da aka girke a gefen hanya a kasar Mali.

Dujarric, ya shedawa taron manema labarai cewa, sun samu bayanin afkuwar lamarin daga ofishin kula da shirin wanzar da zaman lafiya dake Mali, inda aka tabbatar musu da cewa motar MDDr ta gamu da iftila'in ababen fashewa a gefen Boni-Douentza dake yankin Mopti. Ya ce bisa ga bayanan farko da suka samu sun nuna cewa, jami'an kiyayen zaman lafiyar 4 sun mutu sannan wasu 4 sun jikkata.

Mopti yana yankin Inner Niger Delta ne a kasar ta Mali, dake arewa maso yammacin Bamako, babban birnin kasar.

Wakilin musamman na sakatare janar na MDDr, Mahamat Saleh Annadif, yayi Allah wadai da harin.

Kakakin MDDr ya ce, sun bi sahun jami'in wajen mika sakon ta'aziyya ga iyalan wadanda harin ya rutsa da su, kana sun yi fatar samun sauki ga wadanda suka jikkata.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China