in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Manzon musamman na shugaban Sin Xi Jinping ya gana da shugaban kasar Saliyo
2018-05-15 13:40:39 cri
Jiya ne manzon musamman na shugaban kasar Sin Xi Jinping kana ministan kimiyya da fasaha na kasar Sin Wang Zhigang ya gana da shugaban kasar Saliyo Julius Maada Bio a birnin Freetown, babban birnin kasar.

Wang Zhigang ya isar da gaisuwar shugaba Xi Jinping ga shugaba Bio ya kuma mika masa wasikar gayyatar halartar taron koli na dandalin tattaunawa kan hadin gwiwar dake tsakanin Sin da Afirka da za a gudanar a birnin Beijing. Wang Zhigang ya bayyana cewa, a cikin shekaru 47 da kulla dangantakar diplomasiyya tsakanin Sin da Saliyo, kasashen biyu sun dade suna nuna daidaici da goyon baya ga juna, da hada kai tare wajen yaki da cutar Ebola da tinkarar sauran kalubale tare, da kuma hada kan sake gina kasar Saliyo da shimfida zaman lafiya a kasar .

A nasa bangare, shugaba Bio ya bayyana cewa, Saliyo da Sin sun dade suna sada zumunta, kuma sabuwar gwamnatin kasar Saliyo za ta ci gaba da dora muhimmanci ga raya dangantakar dake tsakaninta da kasar Sin, da koyon fasahohin raya kasa daga kasar Sin, da fadada hadin gwiwa da sada zumunta a tsakanin kasashen biyu ta yadda zai amfani jama'arsu baki daya. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China