Sanarwar ta jinjinawa gamayyar kasa da kasa, bisa kokarin da suka yi na ganin kyautatuwar yanayin da ake ciki a zirin Koriya. Shugabannin kasashen nan uku sun yi maraba da ganawar da shugabannin kasashen Koriya ta arewa da ta kudu suka yi a ranar 27 ga watan da ya wuce, kuma suna fatan sassa masu ruwa da tsaki za su ci gaba da kokari, musamman ma game da ganawar da ba da jimawa ba za a gudanar tsakanin shugabannin Koriya ta arewa da Amurka, tare da fatan za a daidaita matsalolin da ke jawo hankalin sassa daban daban, tare da kiyaye kwanciyar hankali a shiyyar.