in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Hukumar yaki da cin hanci ta kasar Sin ta jaddada muhimmancin sanya ido
2018-05-15 09:51:11 cri
Hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta kasar Sin ta bayyana muhimmancin sanya ido da yanke hukunci a sabon zamanin da ake ciki.

Sakataren hukumar Zhao Leji shi ne ya bayyana hakan yayin da yake jawabi a taron karawa juna sani da ya gudana a birnin Chengdu, babban birnin lardin Sichuan dake kudu maso yammacin kasar Sin.

Ya ce, batun yaki da cin hanci shi ne jagora da ruhin sanya ido da yanke hukunci a sabon zamanin da ake ciki, domin kare matsayin Xi Jinping, babban sakataren kwamitin koli na JKS, hukumar kwamitin koli ta JKS da jagororinta.

Jami'in ya kuma bayyana bukatar ganin an aiwatar da ayyukan da aka tsara na shekaru biyar daga shekarar 2018-2022, kana a fadada yadda ake sanya ido zuwa dukkan sassa. (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China