in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin: An hukunta masu laifukan cin hanci da rashawa 159,100 a shekarar 2017
2018-01-08 10:52:45 cri

Hukumar sa ido da ladaftarwa ta kwamitin kolin JKS CCDI, ta ce a shekarar 2017 da ta gabata, ta ladaftar da jami'ai daga sassa daban daban kimanin 159,100, bayan an tabbatar da cewa sun aikata laifuka masu alaka da cin hanci da rashawa ko karya dokokin aikin su.

An tuhumi jami'an ne dai game da batutuwa 122,100, wadanda suka hada da na karya tsare tsaren yaki da fatara na kasar har 48,700. Kaza lika an hukunta wasu jami'an 61,000 bisa laifuka masu nasaba da karya ka'idojin JKS masu alaka da amfani da kudade ko kayan aiki ta hanyoyin da ba su dace ba.

A cewar CCDI a tsakanin watannin Janairu zuwa Nuwambar shekarar ta bara, an kammala hukunce hukunce masu dangantaka da hakan da yawan su ya kai 43,400.

Baya ga wannan kuma, hukumar ta fayyace wasu hukunce hukuncen da aka yanke da yawan su ya kai 670, wadanda suka jibanci karya dokokin jam'iyya da na yaki da cin hanci a shafin ta na yanar gizo, domin hakan ya zama gargadi ga sauran al'ummar kasa.

A daya bagaren kuma, tun daga farkon shekarar 2017, yawan mutanen da suka tserewa shari'a a kasar ta Sin, kana aka samu dawo da su gida sun kai mutum 1,300. Wannan adadi ya kunshi 'yan JKS 347, da jami'an hukumomin kasar, da kuma wasu mutum 14 dake cikin jerin mutane 100 da ake nema ruwa a jallo bisa zargin aikata rashawa.

Alkaluman binciken jin ra'ayin jama'a na shekarar ta 2017 sun nuna cewa, kaso 93.9 bida dari na al'ummar Sinawa, sun gamsu da yadda hukumar ta CCDI ke gudanar da ayyukan ta, adadin da ta haura kaso 75 bisa dari da aka samu a shekarar 2012.(Saminu Alhassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China