in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
CCDI: Yaki da cin hanci ba abu ne mai sauki ba
2017-10-30 11:06:54 cri

Wani rahoton aiki da hukumar ladaftarwa da sanya ido ta kwamitin tsakiyar JKS ta gabatarwa taron wakilan JKS karo 19 da ya kammala a 'yan kwanakin baya, ya ce duk da irin nasarori da hukumar ta CCDI ta cimma a fannin dakile yaduwar cin hanci da rashawa, aikin na cin karo da tarin kalubale.

CCDI ta ce, cikin shekaru 5 da suka gabata bisa ayyukan da take gudanarwa, an cimma nasarar tabbatar da cewa, jami'ai na bin ka'idojin ayyukan hukuma yadda ya kamata. Kaza lika ayyukan jami'iyyar sun kara karfafa, yayin da yanayin ta ke dada samun karsashi da bunkasa.

Rahoton ya kara dacewa, masu aikin tabbatar da da'ar ma'aikata sun binciki jami'ai 440 dake aiki a mataki na larduna, ko ma matsayin da ya zarta haka, game da wasu al'amura masu alaka da cin hanci cikin shekaru 5 din da suka gabata. Cikin su kuwa hadda wasu mambobin kwamitin tsakiya na JKS 43, da wasu ma'aikatan na ita kan ta hukumar ta CCDI.

Rahoton ya kara da cewa, cikin watanni 9 na farkon wannan shekara kadai, an binciki tare da ladaftar da jami'ai 56 dake aiki a matsayin larduna ko sama da haka.

Hukumar ta ce, duk da irin karsashi da wannan aiki ke samu, irin hobbasa da ake yi wajen ganin ya haifar da fa'idar da aka sanya gaba, a hannu guda tushen dake haifar da dabi'ar cin hanci da rashawa na samun gindin zama tsakanin wasu jami'ai. Rahoton ya ce, dabi'u masu barazana ga kyakkyawan yanayin gudanarwar JKS, da raunin shugabancin jam'iyya a wasu sassa, da na cikin manyan kalubale da ayyukan hukumar ta CCDI ke fuskanta.(Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China