in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin ta binciki tsoffin manyan jami'an gwamnati 23 a 2017
2018-01-11 10:40:55 cri

Kimanin tsoffin jami'an gwamnati a matakan larduna ko sama da haka 23 ne suka fada komar hukumomin gabatar da kararraki na kasar Sin a shekarar 2017, babbar hukumar gabatar da kararraki ta kasar wato SPP ce ta sanar da hakan.

Tun a watan Oktoban shekarar 2014, 34 daga cikin 100 na mutane da kasar Sin ke neman su ruwa a jallo ne aka kama, wasu kuma suka yanke shawarar mika kansa da kansu, in ji SPP.

Kasar Sin ta yi hadin gwiwa da kasashen duniya da dama a yunkurinta na maido 'yan kasar da suka tsere kasashen waje bayan da aka zarge su da hannu wajen aikata rashawa. Mafi yawan daga cikin wadanda suka tsere din tsoffin jami'an gwamnati ne ko kuma jami'an wasu kamfanoni mallakar gwamnati.

Tun a shekarar 2017, mutane da suka tsere 1,300 ne suka koma kasar ta Sin bisa radin kansu, daga cikinsu akwai 'yayan jam'iyya kimanin 347 da jami'an ma'aikatu, sannan akwai mutane 14 da aka yada bayanan neman su a matakai na hukumar 'yan sandan kasa da kasa.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China