Taron na yini biyu, zai mai da hankali ne kan batutuwan da suka hada da rawar da gwamnati za ta iya takawa wajen samar da kyakkyawan yanayin kasuwanci da tsaftace harkokin kasuwanci da kuma hadin gwiwa wajen yaki da cin hanci tsakanin kasashen dake cikin shawarar "Ziri daya da hanya daya"
Shawarar "Ziri daya da hanya daya" da kasar Sin ta gabatar a shekarar 2013, na da nufin sake gina hanyar tattalin arziki ta siliki da kuma hanyar Siliki ta cikin ruwa ta karni na 21, bisa hadin gwiwa tsakanin kasashen da ke cikin shawarar domin moriyarsu baki daya, ta hanyar inganta cinikayya ba tare da wani tarnaki ba da kawance a fannin harkokin kudi da samar da kayayyakin more rayuwa da mu'amala ta kut-da-kut tsakanin al'ummominsu. (Fa'iza Mustapha)