in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Morocco ta lashe kofin CHAN na bana bayan da ta doke Najeriya
2018-02-05 10:40:53 cri

Kasar morocco dake karbar bakuncin gasar cin kofin kwallon kafa na 'yan wasan nahiyar Afirka masu wasa a gida ko CHAN a takaice, ta lashe kofin gasar na bana, bayan da ta doke takwararta ta Najeriya da ci 4 da nema, a wasan karshe da suka buga a jiya Lahadi.

Duk dai da rashin kyawun yanayi, dubban 'yan kallo sun ganewa idanun su yadda wasan ya kaya, a filin wasa na sarki Mohammed na 5 dake birnin Casablanca.

Yanzu haka dai Najeriya ta kammala gasar ta bana da lambar azurfa, yayin da kasar Sudan ta samu lambar tagulla, bayan da ta doke kasar Libya da ci 4 da 2 a wasan neman matsayi na 3 da suka buga a ranar Asabar a birnin Marrakech.(Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China