in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Jakada: Kasar Sin tana da niyyar raba nasarorin da ta samu da wasu kasashe
2018-05-14 09:44:33 cri
Jakadan kasar Sin da ke kasar Habasha Tian Jian, ya bayyana a jiya Lahadi cewa, kasarsa ba ta nunawa kasashen Afirka yadda za su gina kansu, amma ya yi imanin cewa, kasashen na Afirka za su iya neman hanyar da ta dace da su.

Da yake yiwa kamfanin dillancin labarai na Xinhua karin haske, Jakada Tan ya ce kasar Sin tana da tabbaci game da hanyar bunkasuwarta, amma hakan ba wai yana nufin tana kokarin tallata tsarin a kasashen katare ba ne. Ya ce, idan har kasashen ketare kawanyensu na sha'awar tsarin, to, a shirye kasar Sin ta ke su ci gajiyar fasahar tare.

Jami'in na kasar Sin ya ce, ba abin mamaki ba ne cewa, wasu kasashen Afirka na fatan koyon nasarorin da kasar Sin ta samu wajen farfado da kanta daga kasa maras karfin tattalin arziki zuwa kasa ta biyu mafi karfin tattalin arziki a duniya.

Ya ce idan kasashen na Afirka suka yi nazarin fasahohin kasar Sin, watakila kasashen Afirkan su koyi yadda kasar Sin ta habaka harkokin ta na zuba jari,raya masana'antu da gina muhimman kayayyakin more rayuwa ta yadda za su dace da ci gabansu.

Koda yake jami'in na kasar Sin ya ce, ba kowane tsari ne ya dace da kowa ba, amma yana fatan cewa, kowace kasa za ta samu hanyar ci gaban da ya dace da yanayinta. Yana mai cewa, kasar Sin ta samu ci gaban tattalin azrikinta ne ta hanyar amfani da shawarwari daban-daban.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China