in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ya kamata a gina dangantaka tsakanin kasar Sin da Afrika bisa matakan rage talauci
2018-04-29 16:31:37 cri
Donald Kaberuka, masanin harkokin tattalin arziki na kasar Rwanda, ya ce kamata ya yi, a gina dangantaka tsakanin kasar Sin da Nahiyar Afrika, bisa matakan rage talauci, la'akari da yadda har yanzu nahiyar ke fuskantar manyan kalubalen da suka shafi talauci.

Donald Kaberuka, ya ce kasar Sin ta yi aiki mai kyau wajen rage fatara, saboda a cikin shekaru 20 da suka shude, matakin raguwar talauci a kasar ya kai kusan rabin matakin na duk duniya.

Ya ce dangantakar tattalin arziki ta fuskar ababen more rayuwa da zuba jari tsakanin kasar Sin da kasashen Afrika abu ne mai kyau matuka, ya na mai cewa ya kamata Afrika ta koyi yadda za ta rage talauci a nahiyar daga gogewa da nasarorin kasar Sin.

A cewarsa, matakin talauci a Afrika na raguwa sosai, kuma cikin shekaru 20 da suka shude, yawancin kasashen nahiyar sun samu nasarori a fannin kiwon lafiya da ilimi da yanayin rayuwa da kuma ci gaban tattalin arziki.

Donald Kaberuka, wanda tsohon Ministan kudi da tsare-tsare ne na Rwanda, ya kara da cewa, duk da wadannan nasarori, har yanzu akwai manyan kalubale, musammam ta fuskar karuwar jama'ar nahiyar.

Bugu da kari, ya ce akwai gibi mai yawa tsakanin birane da kauyuka a fadin nahiyar. Sannan, matakin raguwar talauci bai kai yadda al'ummar nahiyar ke karuwa ba, a don haka, adadin wadanda ke rayuwa cikin talauci ke ci gaba da karuwa. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China