Albert Muchanga ya bayyana hakan ne ga wakilin kamfanin dillancin labarai na Xinhua, bayan da ya halarci zaman mika takardun amincewa da shirin AfCFTA, daga wakilan kasashen Kenya da Ghana a hedkwatar AU.
Ya ce manufar AfCFTA da shawarar ziri daya da hanya daya suna da ma'ana guda, ta bunkasa samar da ababen more rayuwa, da hade sassan kasashen duniya, ta yadda za su rika cin gajiyar juna a fannonin hada hadar cinikayya da hadin gwiwa.
Sauran fannonin da manufofin biyu ke iya taimakawa a cewar jami'in, sun hada da bunkasa harkokin sufuri, da sadarwa, da hade sassan nahiyar da juna. Muchanga ya ce Sin za ta karbi bakuncin taron dandalin hadin gwiwar ta da kasashen Afirka na FOCAC dake tafe cikin watan Satumbar wannan shekara. Yayin da alakar Sin da nahiyar Afirka ke dada fadada ta fuskar cinikayya, taron dandalin na FOCAC dake tafe, zai kara nazartar irin ci gaban da ake samu game hadin gwiwar sassan biyu. (Saminu)