in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Damuwar Amurka kan "Kirar Sin nan da shekarar 2025" ba ta da ma'ana, in ji jakadan Sin
2018-05-13 16:13:38 cri
Kwanan baya, jakadan kasar Sin dake kasar Amurka Cui Tiankai ya bayyana a birnin Washington D.C. cewa, wasu Amurkawa suna nuna damuwa kan manufar "Kirar Sin nan da shekarar 2025", yana mai cewa hakan ba shi da wata ma'ana ko kadan.

A yayin da yake halartar taron kara wa juna sani mai taken "dangantakar dake tsakanin Sin da Amurka a tsawon shekaru 40", taron da cibiyar manyan tsare-tsare da nazarin harkokin kasa da kasa ta kasar Amurka ta kira a ranar 11 ga wata, Cui Tiankai ya bayyana cewa, shirin "Kirar Sin nan da shekarar 2025" babban buri ne da kasar Sin ta sakawa kanta, na neman bunkasuwarta, kuma ba za ta hana sauran kasashen duniya cimma nasu burin ba. A hakika ma dai, ana maraba da dukkan kamfanonin kasar Sin, da na Amurka, har ma da kamfanonin sauran kasashen duniya su shiga wannan shiri.

Bugu da kari, ya ce, a halin yanzu, ana fama da babban matsalar tattalin arziki da cinikayya tsakanin kasar Sin da kasar Amurka, don haka ya kamata kasashen biyu su daidaita sabanin dake tsakaninsu yadda ya kamata. Kaza lika kasar Sin tana fatan Amurka za ta ci gaba da samun wadatar tattalin arziki. A sa'i daya kuma, bunkasuwar tattalin arzikin Sin za ta yi matukar tallafa wa kasar Amurka. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China