in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin ta mayar da martani ga zargin da Amurka ta yiwa kasar Sin
2018-05-09 20:34:41 cri
A ranar 8 ga wata, sabon zaunannen wakilin kasar Amurka dake kungiyar WTO, ya zargi kasar Sin da kasancewa kasa mai ra'ayin bada kariya ga kanta, kana ya ce yana da shakku game da zargin da Sin din ke yi, cewa za ta gamu da wata illa, a sakamakon batun rikicin cinikayya tsakanin ta da Amurka.

Game da wannan, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Geng Shuang ya bayyana yau Laraba cewa, masu salon magana na cewa "Gaskiya ba ta bukatar kwalliya". Kaza lika kasashen duniya na da damar gano wanda ke tabbatar da tsarin ciniki cikin adalci a tsakanin bangarori daban daban, da kuma wanda ke tabbatar da ka'idojin ciniki na duniya. Kana ana iya gane wanda ke daukar matakan bada kariya ga cinikayya, da wanda ke saka takunkumi ga sauran sassa daga bangare daya. Mr. Geng ya ce yana fatan kasar Amurka, za ta daina zargin sauran sassa, kasancewar ita ce ke da hannu a al'amarin.

Geng Shuang ya yi nuni da cewa, yanzu haka an shiga muhimmin lokaci na farfado da tattalin arzikin duniya. Yana kuma fatan kasar Amurka za ta dauki alhakinta, na kasancewa kasa ta farko mai ci gaban tattalin arziki a duniya, da taka rawar da ta dace a duniya. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China