in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Takaddamar ciniki za ta halaka ciniki tsakanin sassan biyu kawai, in ji jakadan Sin dake Amurka
2018-04-20 13:43:21 cri
Bisa gayyatar da cibiyar Fairbank ta jami'ar Harvard ta yi masa, jakadan kasar Sin dake Amurka Cui Tiankai ya yi jawabi a jami'ar a ranar 17 ga wata, inda ya bayyana cewa, ana ciniki tsakanin kasa da kasa domin cimma moriyar juna, takaddamar ciniki za ta haifar da mugun tasiri ga dukkan bangarorin da abin ya shafa, kuma ba zai taimaka wajen warware matsalolin dake gabansu ko kadan ba, illa halaka ciniki a tsakanin bangarori daban-daban daga tushe.

Haka kuma, ya ce, Sin da Amurka suna da bambanci kwarai da gaske a fannoni daban daban, kamar tarihi, al'adu, tsarin siyasa da kuma matsayin samun ci gaba da dai sauransu, ya ce wannan ba abin mamaki ba ne, amma ya kamata a nuna girmamawa da fahimta kan bambancin dake tsakanin kasashen biyu. Kasar Sin ba za ta yi hakuri kan ko wane batu dake shafar kare ikon kanta da kuma kiyaye cikakken zaman yankunan kasar ba, kana, ana fatan za a karfafa shawarwarin dake tsakanin bangarorin biyu kan harkokin ciniki, bisa ka'idojin girmama juna da adalci, ta yadda za a warware sabanin dake tsakanin kasashen biyu yadda ya kamata da kuma cimma moriyar juna.

Haka zalika, ya ce, yadda dangantakar dake tsakanin kasar Sin da kasar Amurka za ta ci gaba, ta danganta sosai kan yadda kasashen biyu suke fahimtar huldar dake tsakaninsu. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China