Manufar wannan matakin ita ce kau da ruwa dake cikin wasu ramuka, musamman ma a dakunan dake karkashin kasa, da lambatu, da wuraren shakatawa, da wuraren da ake gudanar da aikin gine-gine, da cibiyoyin kula da shara, da makamantansu, kamar yadda Liu Zejun, jami'in hukumar kula da lafiya da kayyade iyali na gwamnatin birnin Beijing ya bayyana.
Sauran matakan da za a dauka a wannan karo sun hada da sanya kifaye masu cin sauro a cikin tabkuna, da fesa maganin sauro a wasu wuraren dake da wahalar kawar da ruwa, misali lambatu dake karkashin kasa.(Bello Wang)