in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin na fatan hada kai da Amurka don daidaita sabaninsu
2018-05-10 20:48:29 cri
Yau Alhamis, mai magana da yawun ma'aikatar kasuwancin kasar Sin Gao Feng ya amsa tambayar da aka yi masa, dangane da burin da kasar Sin ke son cimmawa wajen yin shawarwari tare da Amurka, ya ce yana fatan kasashen biyu za su ci gaba da zurfafa mu'amala tsakaninsu bisa tushen girmama juna da yin shawarwari cikin adalci, da inganta hadin-gwiwa, da kuma daidaita sabanin ra'ayi dake tsakaninsu, a wani mataki na kara raya dangantakar kasashen biyu ta fannin tattalin arziki da cinikayya yadda ya kamata.

Gao ya yi wannan furuci ne a yayin taron manema labarai da ma'aikatar kasuwancin kasar Sin ta shirya a yau.

Game da takardar jerin sunayen kayayyakin da Amurka ke shirin sanyawa haraji da ta fitar kwanan baya, Gao ya sake jaddada cewa, kasar Sin ba ta canja matsayinta ba, kuma ba za ta canja ba. Sin na nuna rashin amincewa ga duk wani mataki na bada kariya ga harkokin cinikayya, kana, za ta tsaya haikan kan kare muradun ta da na jama'arta.(Murtala Zhang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China