Da yake bada umarni game da daga darajar kayayyakin, Li keqiang, ya ce daga darajar kayayyakin tare da inganta su, abubuwa ne masu muhimmanci wajen samun ingantaciyyar ci gaba da kuma biyan bukatun jama'a yadda ya kamata, domin samun rayuwa mai nagarta.
Ya ce a shekarun baya-bayan nan, kasar Sin ta samu nasarori a fannin daga darajar kayayyakinta, ya na mai alakanta nasarar da kokarin da dukkan bangarori suka yi.
Ya kara da bukatar hukumomin yankuna da sassan gwamnati, su aiwatar da tsarin inganta kirkire-kirkire da kayyakin da ake sarrafawa da takara tsakanin kamfanoni da samun karin karfi daga 'yan kasuwa masu yawa da kuma amfani da kafar intanet a harkokin masana'antu da kasuwanci.
Har ila yau, Firministan ya ce, yayin da ake kokarin cimma sabbin bukatun jama'a da ci gaba da samun karuwar bukatar kayayyakin a kasuwa akai-akai, ya kamata a kara yawan nau'ikan kayayyaki da kara musu inganci da daraja da inganta kasuwanci da basirar samar da kayyaki, domin kayakin kasar Sin su samu shiga duniya.
An fara gudanar da shirye-shiryen ranar daga darajar kayayyakin kasar Sin, jiya a Shanghai. (Fa'iza Mustapha)