Sa'an nan, dangane da wannan labari, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Geng Shuang, ya furta a yau Talata cewa, an riga an lura da maganar da kasar Amurka ta yi. Haka zalika, jami'in ya jaddada cewa, yadda ake kokarin shawarwari da zummar daidaita sabanin ra'ayi, da kau da rikici, da sanya huldar cinikayya dake tsakanin kasashen Sin da Amurka ta dinga samun ci gaba, ya dace da moriyar kasashen biyu, gami da ta sauran kasashen dake duniyarmu. (Bello Wang)