in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin za ta kare yarjejeniyar kula da batun nukiliyar Iran
2018-05-08 19:19:37 cri
Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Geng Shuang, ya ce, kare yarjejeniyar kula da batun nukiliyar kasar Iran, zai taimakawa kokarin da ake yi na hana yaduwar makaman nukiliya a duniya, da tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a shiyyar gabas ta tsakiya. Saboda haka kasar Sin za ta ci gaba da nuna adalci, da sauke nauyin dake bisa wuyanta, inda za ta kara musayar ra'ayi tare da bangarori masu ruwa da tsaki, da ci gaba da kokarin kare, gami da aiwatar da yarjejeniyar kula da batun nukiliyar Iran.

Kafin haka, shugaban kasar Amurka Donald Trump, ya ce zai sanar da kudurin da ya tsayar game da janyewar kasar Amurka daga yarjejeniyar nukiliyar Iran ko akasin haka cikin kwanaki masu zuwa. Dangane da hakan, wasu manazarta al'amuran yau da kullum na ganin cewa, idan kasar Amurka ta janye daga yarjejeniyar, to, hakan zai kasance kuskure. (Bello Wang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China