Rahoton da kwamitin ya fitar a jiya mai taken, "hasashen harkokin tattalin arziki da zaman al'umman Asiya da tekun Pasifik a shekarar 2018", ya yi nuni da cewa, bunkasuwar kasuwannin cikin gida a kasar Sin za ta samar da zarafi ga abokan cinikinta da ke yankin, yayin da yadda kasar ke kara zuba jari ga kasashen waje, zai taimaka wajen kulla huldar samun moriyar juna da abokan cinikanta.
A wurin taron kaddamar da rahoton, Hamza Ali Malik, jami'in sashen kula da manufofin tattalin arziki da tara jari na kwamitin ya bayyana cewa, kasar Sin na kan gaba a fannin hada-hadar kudi da fasahohi na duniya, kuma kwarewar kasar ta fannin kirkire-kirkire na haifar da tasiri ga sauran kasashen shiyyar. Yana mai cewa, fasahohin da kasar ke da su sun cancanci a yi nazari kansu.(Lubabatu)