Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Geng Shuang, ya taya Putin murnar fara sabon wa'adin aiki a wannan rana. Geng Shuang ya jaddada cewa, Sin ta yi imanin cewa, a karkashin jagorancin shugabannin kasashen biyu, za a kara fadada hadin gwiwar dake tsakanin Sin da Rasha a dukkan fannoni.
A gun taron manema labarun da aka gudanar a wannan rana, Geng Shuang ya jinjinawa dangantakar dake tsakanin Sin da Rasha, yana mai bayyana cewa, a karkashin manufofin da shugaba Xi Jinping da shugaba Putin suka sa kaimin gudanarwa, ana ci gaba da raya dangantakar dake tsakanin kasashen biyu. Ya ce yanzu ana cikin lokaci mafi kyau wajen raya dangantakar abokantaka ta hadin gwiwa bisa manyan tsare-tsare a dukkan fannoni a kasashen biyu. Kaza lika a halin yanzu, Sin da Rasha suna kokarin raya kansu. An kuma yi imanin cewa, za a kara zurfafa dangantakar abokantaka a tsakaninsu a sabon lokaci, da kuma kara fadada hadin gwiwarsu a dukkan fannoni. (Zainab)