in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Manyan jami'an Sin da Amurka sun yi musayar ra'ayi
2018-05-06 16:41:59 cri
Mista Yang Jiechi, mamban kwamitin siyasa na tsakiyar jam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin, ya yi musayar ra'ayi da sakataren harkokin wajen Amurka, Mike Pompeo ta wayar tarho a jiya Asabar.

Yayin zantawar, mista Yang Jiechi ya ce, huldar dake tsakanin Sin da Amurka, na cikin wani lokaci mai muhimmanci sosai. Kuma kamata ya yi, bangarorin 2 su yi kokarin aiwatar da ra'ayi daya da shugaban kasar Sin Xi Jinping da takwaransa na Amurka Donald Trump suka cimma, da karfafa mu'amalar da ake yi tsakanin manyan kusoshi da sauran jami'an kasashen 2, da kara kokarin musayar ra'ayi bisa batutuwan da suka hada da tattalin arziki da cinikayya, da girmama juna bisa babbar moriyarsu da abubuwan da suke mai da hankali a kai, da daidaita sabanin ra'ayinsu, da kara yin musayar ra'ayi tsakanin kasashen 2 bisa wasu manyan batutuwan kasa da kasa da na wasu shiyyoyi, ta yadda za a samu damar cimma burin ciyar da huldar dake tsakaninsu gaba.

A nasa bangaren, mista Pompeo ya ce Amurka da Sin kasashe ne masu karfin tattalin arziki da za su iya hadin gwiwa da juna a fannoni daban daban. Ya ce Amurka na da yunkurin raya huldar da ke tsakanin kasashen 2 muhimmanci sosai. Ana fatan bangarorin 2 za su kara yin musayar ra'ayi kan hanyoyin da za a iya bi domin raya huldar dake tsakaninsu.(Bello Wang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China