in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Xi Jinping ya nuna kyakkyawan fata ga matasa a sabon zamanin da ake ciki
2018-05-03 13:20:30 cri

A yayin da ake murnar Ranar 4 ga watan Mayu, wato Ranar Matasan kasar Sin da murnar cika shekaru 120 da kafuwar jami'ar Peking ta kasar, babban sakataren kwamitin tsakiya na jam'iyyar kwaminis ta Sin, kuma shugaban kasar Xi Jinping ya kai ziyara a jami'ar Peking. A madadin kwamitin tsakiya na jam'iyyar kwaminis ta Sin, Xi Jinping ya taya wa dukkan malamai da dalibai na jami'ar, da matasan kabilu daban daban na kasar Sin, da kuma ma'aikata wadanda suke yi aiki game da harkokin matasa na kasar murnar wannan Ranar Matasan kasar Sin. Xi Jinping ya jaddada cewa, ya kamata matasa su yi kokarin zama muhimmin karfi wajen farfado da al'ummar kasar Sin da ci gaban kasar, da kuma kabilu daban daban. Kana jami'o'i su horar masu yadda za a tsaya kan matsayin bin tsarin gurguzu, da bin tafarkin siyasa da ya dace, da horar da nagartattun malamai da kafa tsarin horar da kwararru mai inganci, da raya wasu jami'o'in da za su zama jami'o'i mafi kyau a duk fadin duniya.  

A ranar 2 ga wata da tsakar rana, daliban jami'ar Peking suka marabaci shugaba Xi Jinping a jami'arsu. Daliban da suka tsaya a gefen hanya sun yi musabaha da shugaba Xi Jinping, inda suke fadan cewa "hada kai domin farfado da kasar Sin" tare.

Wannan ne karo na 6 da shugaba Xi Jinping ya kai ziyara jami'ar Peking. An bullo da tunanin kishin kasa da neman ci gaba da kuma shimfida demokuradiyya da yada ilmin kimiyya bayan gwagwarmayar da aka yi a ranar 4 ga watan Mayu na Shekarar 1919, wadda ta bude shafin shimfida sabuwar demokuradiyya a kasar Sin, da kokarin yada tunanin Markisanci a kasar, da kafuwar jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin. A matsayin wurin kaddamar da wannan gwagwarmaya, jami'ar Peking ta kalli wannan tarihin da ya faru yau kusan shekaru 100 da suka gabata.

Xi Jinping ya jaddada cewa, dole ne jami'o'i sun samu ci gaba a yayin da kasarmu take samun ci gaba. Kasar Sin tana bukatar nagartattun jami'o'in da suke da halin musamman na kasar Sin, kuma suka yi suna a duk fadin duniya.

Jami'ar Peking ta riga sauran kafofi wajen yada da kuma nazarin tunanin Markisanci a kasar Sin. Shekarar bana shekara ce ta cika shekaru 200 da aka haifi Karl Heinrich Marx, kana shekaru 170 ne da aka wallafa "Sanarwar Jam'iyyar Kwaminis". Xi Jinping ya jaddada cewa, abin da ake yi don tunawa da Markisanci da "Sanarwar Jam'iyyar Kwaminis" shi ne a yi nazari da yada tunanin taron wakilan jam'iyyar kwaminis ta Sin karo na 19 da tunanin tsarin gurguzu mai alamar kasar Sin a sabon zamanin da ake ciki yadda ya kamata. Xi Jinping ya ca a nazarci yadda duniya da kasar Sin da ma jam'iyyar ke ciki, kana a nazarci tsarin gurguzu mai alamar kasar Sin a sabon zamani, sannan a gabatar da sakamakon nazari mai inganci da zai samu amincewa daga bangarori daban daban. Xi ya bayyana cewa,  

"Matasa ba ma kawai masu kafa buri ba ne, har ma su masu neman cimma buri ne. Wadanda suke kafa buri suna bukatar kuzari da burinsu, amma wadanda suke kokarin cimma burinsu suna bukatar yin kokari da ba da gudummawarsu. Ya kamata matasa su zauna jarraba yayin da suke yin kokarin neman cimma buri don samar da gudummawa wajen farfado da al'ummar kasar Sin da raya kasar Sin baki daya."

Xi Jinping ya jaddada cewa, ya kamata a tsaya tsayin daka wajen bin tsarin gurguzu mai alamar kasar Sin, da raya kasar Sin ta zamani, don haka ana bukatar matasa su yi kokarin cimma wannan buri. Yanzu cikin gaggawa ne ana bukatar ilmin kimiyya da nagartattun kwararru da nagartattun jami'o'in domin bunkasa harkokin kasar Sin. Xi Jinping ya jaddada cewa,

"Dukkan kasashen da suka samu karfi ne sakamakon nagartattun mutane, duk wanda ya zama kwararre ne sakamakon ilmin da ya koya. Horar da dalibai wadanda za su iya bin tsarin gurguzu, da kuma bunkasa shi ka'ida ce da jam'iyyarmu ta Kwaminisanci ta kasar Sin take bi, kuma nauyi ne da aka dora wa dukkan makarantu da kwalejoji da kuma jami'o'i na kasarmu. Jami'o'i na taka muhimmiyar rawa wajen horar da matasa. Ya kamata jami'o'i su horar da matasan da za su raya tsarin gurguzu, ta haka za a samu jami'o'i masu kyau masu alamar kasar Sin a duniya."

Xi Jinping ya kuma nuna cewa, ya kamata jami'o'in kasar Sin su horar da wadanda za su raya tsarin gurguzu, da bin tafarkin siyasan da ya dace, da horar da malamai da bullo da tsarin horar da nagartattun kwararru, da raya jami'o'i masu alamar kasar Sin a duniya. Xi ya ce,  

"A sabon zamanin da ake ciki, ya kamata matasa su yi kokarin neman cimma burinsu da raya tsarin gurguzu mai alamar kasar Sin, da kokarin raya zamantakewar al'ummar kasa mai wadata, da raya kasar Sin ta zamani mai karfi, da kuma farfado da al'ummar kasar Sin." (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China