in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya sanar da sabbin matakan zurfafa yin gyare-gyare a gida daga dukkanin fannoni
2018-04-13 23:26:56 cri


An yi kasaitaccen bikin cikar lardi na Hainan, da yankin tattalin arziki na musamman na Hainan shekaru talatin da kafuwa a yau Jumma'a, inda shugaban kasar Sin Xi Jinping, wanda kuma shi ne babban sakataren kwamitin koli na jam'iyyar kwaminis ta kasar, kuma shugaban kwamitin koli na sojin kasar, ya gabatar da muhimmin jawabi. Xi ya jaddada cewa, ya zama dole a ci gaba da kafa yankunan raya tattalin arziki na musamman, tare da kara habaka su. Shugaba Xi ya kuma ce, a halin da ake ciki, ya kamata lardin Hainan ya yi kokarin kafa yankin gwaji na gudanar da cinikayya maras shinge, gami da cibiyar fiton kayayyaki ta gudanar da ciniki cikin 'yanci mai salon musamman na kasar Sin, da kuma raya yankin gwaji na zurfafa yin gyare-gyare a gida da bude kofa ga kasashen waje, da yankin gwaji na kiyaye muhallin halittu, da cibiyar yawon shakatawa ta duniya, da yankin bada tabbaci ga manyan tsare-tsare na kasa, har ya zama wani kyakkyawan abun misali da zai nuna martabar kasar Sin a idon fadin duniya baki daya.

A cikin jawabin da Xi ya gabatar, ya ce, ya kamata a maida hankali kan bude kofa ga kasashen waje yayin da ake kokarin habaka lardin Hainan, inda ya ce:

"Kwamitin tsakiya na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin ya yanke shawarar raya lardin Hainan, ta yadda zai zama yankin gwaji na gudanar da cinikayya cikin 'yanci, da nuna masa goyon-baya wajen raya cibiyar fiton kaya ta gudanar da ciniki cikin 'yanci mai halayya ta musamman na Sin. Jam'iyyar kwaminis din ta yanke muhimmiyar shawarar ne bisa la'akari da halin da ake ciki a gida da waje, wanda ya kasance wani babban matakin da gwamnatin kasar Sin ta dauka wajen fadada bude kofa ga kasashen ketare, gami da kara dunkule tattalin arzikin duniya baki daya."

Shugaba Xi ya kuma bayyana cewa, yayin da ake kokarin gina cibiyar fiton kaya ta gudanar da cinikayya cikin 'yanci a lardin Hainan, dole ne a yi koyi da nasarorin da sauran wasu kasashen duniya suka samu a wannan fanni. Xi ya ce:

"Muna maraba da daukacin masu zuba jari daga dukkanin sassan duniya, su shiga hada-hadar kasuwanci a lardin Hainan, da gina cibiyar fiton kaya ta gudanar da cinikayya cikin 'yanci, ta yadda kasashe daban-daban za su ci gajiyar damammakin samar da ci gaba da sakamakon sauye-sauyen da kasar ke aiwatarwa."

Shugaba Xi ya jaddada cewa, ya zama dole lardin Hainan ya nuna kwazo wajen raya fasahohin zamani na sadarwa, da kara inganta ababen more rayuwar al'umma, don hada lardin da sauran sassan duniya, da kuma habaka ayyukan gona, da zurfafa binciken yankin teku. Shugaba Xi ya sake nanata cewa, ya kamata lardin Hainan ya zama jagora a duk fadin kasar Sin, wajen yin kwaskwarima ga tsarin kiyaye muhallin halittu, inda ya ce:

"Kwamitin tsakiya na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin na goyon-bayan lardin Hainan don gina yankin gwaji na kiyaye muhallin halittu na kasa, abun dake bukatar daukar tsauraran matakai na kiyaye muhalli halittu. Ya kamata Hainan ya kafa tsarin sa ido kan ayyukan kiyaye muhallin halittu na zamani gami da na kiyaye albarkatu, da kuma gina lambun shan iska na kasa. Har wa yau, ya kamata a tsaurara matakan kiyaye muhallin teku."

Har ila yau, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya nuna cewa, gwamnatin kasar Sin na nunawa lardin Hainan goyon-baya wajen kara jawo hankalin kwararru da masana daga sassan duniya, inda ya ce:

"Za mu amince da kwararru masu fasaha daga kasashen waje ko kuma daga yankunan Hongkong da Macau da Taiwan don su samu ayyukan yi har su iya zaman dindindin a lardin Hainan, da bada izini ga daliban kasashen waje wadanda suka samu digiri na biyu ko kuma fiye da haka a jami'o'in kasar Sin don su raya sana'o'insu a Hainan. Ya kamata lardin Hainan ya kafa tsarin jawo masana kimiyya da fasaha daga kasashen ketare, da kyautata tsarin shigo da irin wadannan mutane, ta yadda za su iya bada gudummawarsu a lardin Hainan."(Murtala Zhang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China