in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaba Xi Jinping ya gana da manyan kushoshin wasu kasashe mahalarta taron dandalin Boao
2018-04-11 14:15:30 cri

Bayan ya halarci bikin kaddamar da taron shekara-shekara na dandalin tattaunawa tsakanin kasashen Asiya na Boao na bana, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gana da wasu manyan kusoshin kasashe mahalarta taron a garin Boao da yammacin jiyan, wadanda suka hada da firaministan kasar Holland Mark Rutte da firaministan kasar Pakistan Shahid Khaqan Abbasi da kuma shugaban kasar Philippines Rodrigo Duterte. Inda yadda za a hada kai bisa shawarar "Ziri daya da Hanya daya" ya zama batun da ya ja hankulan bangarori daban daban.

Da yammacin jiya Talata ne shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gana da firaministan kasar Holland Mark Rutte a garin Boao na lardin Hainan da ke kudancin kasar Sin. Wannan shi ne karo na hudu da shugabannin biyu ke ganawa. A farkon ganawar, Shugaba Xi Jinping ya ambaci jawabin da Mr. Rutte ya bayar a yayin taron dandalin tattaunawar Boao, inda ya ce ,

"Jawabin da ka yi a yayin taron dandalin tattaunawar Boao na da kyau sosai, inda ka jaddada matsayin kasarka ta Holland na ci gaba da goyon bayan tsarin yin cinikayya tsakanin bangarori daban daban kamar yadda kungiyar WTO ke yi, da yayata tsarin gudanar da cinikayya maras shinge, da kuma yaki da ra'ayin ba da kariyar cinikayya. Game da wannan batu, Sin da Holland, na da ra'ayi da matsayi kusan iri daya, don haka bangarorin biyu za su iya inganta hadin kansu. Bugu da kari, na yaba maka kan yadda ka bayyana cewa, Holland za ta sa kaimi ga hadin gwiwar Sin da Turai bisa shawarar 'Ziri daya da Hanya daya'. Muna son yin kokari tare da Holland don daga dangantakar da ke tsakanin kasashen biyu zuwa wani sabon mataki."

A nasa bangaren, Mr. Rutte ya ce, dangantakar da ke tsakanin Holland da Sin na da karfi da kuma matukar muhimmanci. Kasarsa na sa ran ganin samun ingantuwar hadin kai, da raya abota bisa shawarar "Ziri daya da Hanya daya" don moriyar juna da samun nasara tare.

Yayin da yake ganawa da firaministan kasar Pakistan Shahid Khaqan Abbasi, Shugaba Xi Jinping ya nuna cewa, kasar Sin na son hada hannu da Pakistan wajen yada zumuntar gargajiya, da mara baya ga juna da kula da muradunsu na bai daya, domin raya makoma ta bai daya a tsakanin kasashen biyu. Xi ya kara da cewa,

"Tun bayan ziyarar da na kai Pakistan a shekarar 2015, ake raya dangantakar abota tsakanin Sin da Pakistan bisa manyan tsare-tsare daga dukkan fannoni yadda ya kamata. Lamarin da bai tsaya ga sa kaimi ga ci gaba da tsaron kasashen biyu ba, har ma ya bayar da gudummawa ga samun zaman lafiya da na karko da wadata a shiyya-shiyya. Ya kamata huldar da ke tsakanin kasashen biyu ta zama abin koyi na yadda ake raya zumunta a tsakanin kasashen da ke makwabtaka da juna, da ginshiki a fannin zaman lafiya da kwanciyar hankalin shiyya-shiyya da ma kyakkyawan misali na hadin gwiwar kasa da kasa bisa shawarar 'Ziri daya da Hanya daya'."

A nasa bangaren kuma, Mr. Abbasi ya furta cewa,

"Pakistan da Sin aminai ne, a nan ina so in nanata cewa, Pakistan ta tsaya kan manufar kasancewar kasar Sin daya tak a duniya, kuma za ta nuna wa Sin goyon baya sosai a kan batutuwan da suka shafi babbar moriyarta da manyan lamuran da ke daukar hankalinta."

Shugaban kasar Philippines Rodrigo Duterte shi ne bako na karshe da Shugaba Xi ya gana da shi a jiya. A farkon ganawarsu, Xi ya girmama huldar da ke tsakanin kasashen biyu a cikin shekaru biyu da suka gabata, inda ya ce, an daga huldar har zuwa matakai biyu, wato daga samun kyatatuwa zuwa hulda mai karfi. Xi ya kuma kara da cewa,

"Ina ganin ci gaban huldar da ke tsakanin Sin da Philippines a halin yanzu, ina son hadin kai wajen kiyaye dankon zumunci a tsakaninmu, da kafa burinmu na samun bunkasa tare, gami da warware sabani bisa basira, a kokarin tabbatar da raya huldar yadda ya kamata."

A nasa bangaren kuma, Shugaba Duterte ya ce, kasarsa na da niyyar sa hannu cikin shirin raya hanyar siliki na kan teku na karni na 21, da inganta hadin gwiwa tare da Sin a fannonin tattalin arziki da cinikayya, da yawon shakatawa da ba da ilmi da raya manyan ababen more rayuwa, da aiwatar da doka, da kuma tsaro. Kana kasarsa za ta kokarta tare da Sin don kiyaye zaman karko a tekun kudancin kasar Sin ta hanyar shawarwari, ta yadda tekun zai zama wani fannin da kasashen biyu za su iya hadin gwiwa a kai. (Kande Gao)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China