in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Xi Jinping: Sin ta kiyaye yin kwaskwarima
2018-04-12 10:49:13 cri

A ranar 11 ga wata da safe, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gana da membobin majalisar dandalin tattaunawa na Asiya na Boao da membobin majalisar masu jiran gado, tare da yin shawarwari tare da wakilan masu ciniki na Sin da na kasashen waje wadanda suke halartar taron dandalin tattaunawar. A gun shawarwarin, Xi Jinping ya jaddada cewa, Sin ta kiyaye yin kwaskwarima, ba a gama aikin yin kwaskwarima ba, ta kiyaye bude kofa ga kasashen waje, da yin maraba da kasa da kasa su more fasahohin Sin na kwaskwarima da bude kofa da samun bunkasuwa.

"Masu ciniki da suke yin shawarwarin a nan, su 26 cikinku da wadanda suka zo daga kasar Sin, ciki har da yankin Hongkong da yankin Macau, wasu guda 11 cikinsu sun zo ne daga kasashe daban na nahiyar Asiya, sannan wasu 14 kuma daga cikinku sun zo ne daga sauran kasashen Turai da Amurka…"

A ranar 11 ga wata da safe, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya yi shawarwari tare da masu ciniki na Sin da waje 51 wadanda suke halartar taron shekara-shekara na dandalin tattaunawa na Asiya na Boao na shekarar 2018, ciki har da shugaban kamfanin Charoen Pokphand na kasar Thailand, da wakilan kungiyar ciniki ta Amurka, da shugaban kamfanin motoci na Toyota na kasar Japan da sauransu. Xi Jinping ya bayyana a yayin shawarwarin cewa,

"Na yi farin ciki da ganawa da ku masu ciniki. Ta wannan taro, gwamnatin kasar Sin za ta iya yin mu'amala da masu ciniki na Sin da waje kai tsaye, kana ana iya sauraron ra'ayoyi da shawarwari, yana da babbar ma'ana gare mu. Dandalin tattaunawa na Asiya na Boao dandali ne na tattalin arziki, ra'ayoyin da aka bayar a gun dandalin tattaunawar suna da muhimmanci sosai. Masu ciniki sun halarci dandalin tattaunawar wadanda suka samar da gudummawa ga bunkasuwar dandalin tattaunawar a shekaru 17 da suka gabata."

A gun shawarwarin, Xi Jinping ya jaddada cewa, Sin ta kiyaye yin kwaskwarima da kanta, ba a gama aikin yin kwaskwarima ba, kana ta kiyaye bude kofa ga kasashen waje. Sin ta tsaya tsayin daka kan raya tattalin arzikin duniya na bude kofa, da samar da gudummawarta ga bunkasuwar nahiyar Asiya har ma da dukkan duniya baki daya. Sin tana maraba da kasa da kasa su more fasahohinta a fannonin yin kwaskwarima da bude kofa da kuma samun bunkasuwa. Xi ya ce,

"A bara, Sin ta gudanar da taron wakilan jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin karo na 19 cikin nasara. A watan Maris na bana, Sin ta gudanar da manyan taruruka biyu cikin nasara. Abin da muke fada ya yi kamar yadda na bayyana a jiya, wato an shaida cewa, Sin za ta ci gaba da yin kwaskwarima da bude kofa ga kasashen waje. Za a kyautata tsarin kasar Sin, da samun bunkasuwa mai inganci, da sarrafa kasa yadda ya kamata, ta haka jama'ar kasar Sin za su ji dadi da tabbatar tsaro."

Xi Jinping ya bayyana cewa, Sin za ta kara samar da yanayi mai kyau ga masu ciniki na Sin da na kasashen waje a fannin zuba jari da kafa kamfanoni. Yana fatan masu ciniki za su kara samar da gudummawa da samun bunkasuwa yayin da Sin take yin kwaskwarima da bude kofa ga kasashen waje a sabon lokaci.

Masu ciniki mahalarta shawawarin sun bayyana cewa, sabbin matakan fadada bude kofa ga kasashen waje da shugaba Xi Jinping ya gabatar a gun bikin bude taron dandalin tattaunawa na Asiya na Boao sun sa kaimi ga raya yunkurin bunkasa duniya bisa tsarin bai daya, za su rike dama da shiga yunkurin yin kwaskwarima da bude kofa ga kasashen waje na kasar Sin, da raya shawarar "ziri daya da hanya daya", da sa kaimi ga bunkasa kamfanoni da samun wadata a nahiyar Asiya har ma a duniya gaba daya.

Shekarar bana shekara ce ta canja mambobin majalisar dandalin tattaunawa na Asiya na Boao, tsohon babban sakataren MDD Ban Ki-moon ya zama sabon shugaban majalisar dandalin tattaunawar, mataimakin shugaban majalisar bada shawara kan harkokin siyasa ta kasar Sin karo na 12 kuma tsohon gwamnan babban bankin kasar Sin Zhou Xiaochuan ya zama babban wakilin Sin dake dandalin tattaunawar kuma mataimakin shugaban majalisar dandalin tattaunawar. A ranar 11 ga wata, shugaba Xi Jinping ya gana da mambobin majalisar dandalin tattaunawa na Asiya na Boao da mambobin majalisar masu jiran gado, ya ce,

"A shekarun baya bayan nan, shugaban majalisar dandalin tattaunawar Yasuo Fukuda, da mataimakin shugaban majalisar Zeng Peiyan, sun yi kokari tare da sauran membobin majalisar da gabatar da ra'ayoyi da shawarwari kan manyan batutuwan tattalin arzikin Asiya da na duniya, wadanda suka samar da gudummawa sosai. Na yi imani cewa, a karkashin jagorancin sabon shugaban majalisar Ban Ki-moon da mataimakin shugaban majalisar Zhou Xiaochuan, sabbin membobin majalisar za su sa kaimi wajen gudanar da ayyukan dandalin tattaunawar yadda ya kamata, da samar da sabuwar gudummawa ga shimfida zaman lafiya da samun bunkasuwa a Asiya har ma ga duniya a sabon lokaci." (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China