in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sakwanni uku da shugaban kasar Sin ya isar ga duniya a jawabin da ya gabatar a taron dandalin Boao
2018-04-10 20:02:15 cri
A yau Talata, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar da jawabi, a gun taron shekara shekara na dandalin Boao na kasashen Asiya, inda ya gabatar da muhimman matakan da kasarsa za ta dauka, ta fannin kara bude kofarta ga kasashen waje. Baya ga kasancewar matakan da za a dauka wata hanya ta kara bude kofar kasar Sin ga ketare cikin sabon zamani, haka kuma za su samar da damar farfado da tattalin arzikin kasashen duniya.

Kara bude kofa ga kasashen duniya

Bana shekara ce ta cika shekaru 40 da kasar Sin ta fara aiwatar da manufar yin gyare-gyare a gida, da kuma bude kofa ga kasashen waje. A jawabin da ya gabatar, shugaba Xi Jinping ya waiwayi nasarorin da kasar ta cimma cikin shekaru 40 da suka wuce. Ya ce cigaban tattalin arziki da fid da al'umma sama da miliyan 700 daga kangin talauci, da kuma samar da gundumar da ta kai sama da kaso 30% na ci gaban tattalin arzikin duniya, dukkaninsu nasarori ne da suka shaida muhimmancin matakin ta fannin tabbatar da makomar kasar, da kuma warware matsalar ci gaban tattalin arzikin duniya.

Sai dai akwai sauran rina a kaba a farfadowar tattalin arzikin duniya, inda kariyar ciniki ke ci gaba da kawo rashin tabbas, don haka kasashen duniya na fatan kasar Sin za ta ci gaba da samar da tabbashi, da kuzari bisa ga gyare-gyaren da take yi.

A jawabin da shugaban ya gabatar, ya yi alkawarin cewa, "al'ummar kasar Sin za su ci gaba da kokartawa da gudanar da gyare-gyare, kuma za a tsaya tsayin daka a kan karfafa yin gyare-gyare a gida". "kasar Sin a maimakon ta rufe kofarta, za ta kara bude ta ga kasashen duniya", "kasar Sin za ta rika kasancewa mai kiyaye zaman lafiyar duniya, kuma mai ba da taimako ga bunkasuwar duniya, kuma mai kiyaye tsarin duniya."

Sanar da sabbin matakan bude kofa, da maraba da neman ci gaba sakamakon ci gaban kasar Sin

Yanzu haka, kasar Sin ta canza matakinta na bunkasa tattalin arziki daga samun saurin bunkasuwa, zuwa samun bunkasuwa mai inganci. Hakan ya sa dole ne kasar Sin ta kara inganta bude kofarta ga kasashen ketare, wannan ba domin biyan bukatun kasar Sin kawai ba ne, har ma don samar da alheri ga duniya sakamakon dunkulewar tattalin arzikin duniya. To, ko ta yaya za a kara bude kofa ga kasashen ketare?

Shugaba Xi Jinping ya sanar da manyan matakai a fannoni guda hudu a yayin jawabinsa: wato kara fadada hanyoyin shiga kasuwannin kasar Sin, da kyautata muhallin jawo jarin waje, da kara kiyaye hakkin mallakar ilmi, da kuma kara shigar da kayayyaki.

Game da manufofin cinikayya da zuba jari na kasar Sin, kullum kafofin watsa labarun kasashen yamma na fahimtar kuskure, da yin zargi a kai, bisa matsayin moriyarsu. Amma, sabon ra'ayin da shugaba Xi Jinping ya nuna ya baiwa kafofin watsa labarun duniya wata amsa mai tabbaci, wato ko da yaushe kasar Sin na kokarin yi wa kanta kwaskwarima, tana amfani da yin kwaskwarima wajen inganta bude kofa ga kasashen ketare, kana da amfani da bude kofa ga kasashen ketare wajen gaggauta yin kwaskwarima.

An yi hasashen cewa, wadancan sabbin matakai na bude kofa ga kasashen ketare, ba kawai za su kara saurin kafa tsarin tattalin arziki na zamani na kasar Sin ba ne, har ma za su samar da babbar dama mai kyau ga ci gaban kasashe daban daban. Ayyukan yin kwaskwarima da bude kofa ga kasashen ketare da Sin ke yi na tsawon shekaru 40, sun nunawa Sin da duniya cewa, sai an yi haka ne kasar Sin da duniya baki daya za su iya samun wadata da albarka.

Amsa tambayoyin da wannan zamaninmu ya kawo, da kafa alkibla ga ci gaban kasashen duniya

Ci gaban kimiyya da fasaha na zamani gami da kwaskwarimar da ake ta fuskar masana'antu, na haifar da sabbin damammaki ga zaman rayuwar al'umma. A waje guda kuma, yake-yake da cututtuka, da zaman fatara da kuma matsalar sauyin yanayi, na ci gaba da kawo barazana ga zaman rayuwar al'umma. To, ko mece ce makomar bil'adama? Mece ce kuma makomar nahiyar Asiya?

Shugaba Xi Jinping ya amsa wadannan tambayoyi ta hanyar takaita manyan nasarorin da kasar Sin ta samu, sakamakon manufar yin gyare-gyare a gida da bude kofarta ga kasashen waje da ta fara aiwatarwa shekaru arba'in da suka wuce, inda ya ce, idan wata kasa ko wata kabila na son samun farfadowa da ci gaba, ya zama dole ta mutunta tarihi tare kuma da bin yayi. Shugaba Xi ya ambaci wasu muhimman fannoni uku, wadanda suka hada da, yin hadin-gwiwa cikin zaman lafiya, da bude kofa, da yin mu'amala da sauran kasashe, gami da yin kwaskwarima da kirkire-kirkire, abun da ya lalubo bakin zaren daidaita matsalolin da kasashe daban-daban ke fuskanta, yayin da suke kokarin neman samun ci gaba.

Kowane zamani na fuskantar matsala, kowace zuriya na da nata nauyi na musamman

A shekara ta 1978, kasar Sin ta fara aiwatar da manufar yin gyare-gyare a gida da bude kofa ga kasashen waje. A shekarar bana wato 2018, a lardin Hainan, shugaba Xi Jinping ya kaddamar da sabbin matakai na yin gyare-gyare a gida da bude kofa ga kasashen ketare.

Ya kamata kasa da kasa su fahimci cewa, yin gyare-gyare a gida da bude kofa ga kasashen waje da kasar Sn za ta yi a wannan zamanin da muke ciki, ba zai kawo barazana ga sauran kasashe ba. Makasudin yin hakan shi ne, domin cimma muradun al'ummar kasar Sin, da na duk fadin duniya baki daya. Babu shakka, kasar Sin za ta iya bayar da babbar gudummawa ga ci gabanta, da na nahiyar Asiya da ma duk duniya baki daya! (Lubabatu bilkisu Murtala)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China