in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
MDD ta yi matukar takaici bisa harin biranen Kabul da Kandahar
2018-05-01 15:44:25 cri
Babban magatakardar MDD Antonio Guterres, ya bayyana matukar takaicin sa, game da hare haren ta'addanci da aka kaddamar a biranen Kabul da Kandahar na kasar Afghanistan. Yana mai gabatar da ta'aziyyar sa ga iyalan wadanda hare haren suka rutsa da su.

Da yake bayyana hakan ga menema labarai a jiya Litinin, kakakin sa Stephane Dujarric, ya ce hare haren sun haddasa rasuwar fararen hula da dama, ciki hadda ma'aikatan ba da agajin gaggawa, da yara 'yan makaranta.

Da sanyin safiyar ranar Litinin ne dai wasu 'yan kunar bakin wake su 2, suka tada wani bam a unguwar jami'an diflomasiyya dake tsakiyar birnin Kabul, lamarin da ya sabbaba rasuwar a kalla mutane 23, ciki hadda maharani su 2, baya ga wasu mutanen 27 da suka jikkata.

Kaza lika wata fashewar ta auku a unguwar Daman dake lardin Kandahar na kudancin kasar, harin da ake zaton an kitsa shi ne domin hallaka wani jerin gwanon rundunar sojojin kasar. Sai dai rahotanni sun ce harin ya hallaka fararen fula ne su 11, baya ga wasu da dama da suka jikkata.

Kungiyar 'yan jarida ta Afghanistan ta ce, cikin wadanda harin Kabul ya rutsa da su hadda wasu 'yan jarida su 9. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China