in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kwamitin sulhun MDD ya yi Allah wadai da farmaki da aka kai a Kabul
2018-01-28 13:53:59 cri
Jiya ranar Asabar, kwamitin sulhun MDD ya bayar da sanarwa, inda ya yi suka sosai kan harin kunar bakin wake da aka tayar a cibiyar birnin Kabul, babban birnin kasar Afghanistan, kana ya aike da sakon jajantawa ga iyalan wadanda suka mutu da ma gwamnatin kasar.

A cikin sanarwar kwamitin ya jaddadda cewa, dole ne a hukunta wadanda suke bada taimakon kudi da goyon baya ga ayyukan ta'addanci da kuma wadanda suka aikata ayyukan, a sa'i guda ya kalubalanci dukkan kasashen duniya dasu hada kai tare da gwamnatin kasar Afghanistan da wasu bangarorin da abin ya shafa don sauke nauyin dake wuyansu, kamar yadda aka tanada cikin dokokin kasa da kasa da kudurorin kwamitin sulhun MDD.

Baya ga haka, kwamitin sulhun ya sake nanata cewa, duk wani irin ayyukan ta'addanci kalubale ne mafi tsanani dake kawo barazana ga zaman lafiya da tsaron kasa da kasa, tilas ne duk kasashen su yi iyakacin kokarin magance su. (Bilkisu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China