in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Babban sakataren MDD ya yi tir da farmaki da aka kai a babban birnin Afghanistan
2018-01-28 12:54:35 cri
Jiya ranar Asabar, babban sakataren MDD Antonio Guterresm, ya fidda wata sanarwa ta bakin kakakinsa, inda ya yi Allah wadai da harin kunar bakin wake da aka tayar a cibiyar birnin Kabul, babban birnin kasar Afghanistan.

A cikin sanarwar, kakakinsa Stéphane Dujarric ya ce, farmakin da aka kai ga fararen hula aiki ne na take hakkin bil Adama da dokokin jin kai na kasa da kasa, dole ne a hukunta wadanda suka kaddamar da harin.

Harin dai ya haddasa rasuwar mutane a kalla 95, tare da raunata mutane 163. Mai yiwuwa ne adadin mutanen da suka rasu zai iya karuwa, kasancewar wasu da dama sun samu raunuka masu tsanani. Kungiyar mayakan Taliban ta Afghanistan ta sanar da daukar alhakin kaddamar da harin.

Wannan ne babban farmaki na biyu da kungiyar mayakan na Taliban ta Afghanistan ta kaddamar a Kabul a cikin wannan wata. A ranar 20 ga wata, kungiyar mayakan na Taliban ta kai farmaki kan wani otel a birnin Kabul, a sakamakon haka, mutane a kalla 22 sun rasa rayukansu, ciki har da baki 'yan kasashen waje 14. (Bilkisu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China