in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kura ta lafa bayan hari kan hotel din a Kabul
2018-01-22 13:42:16 cri
A jiya Lahadi, ma'aikatar harkokin cikin gida ta kasar Afghanistan ta bayyana cewa, bayan sa'o'i fiye da 10 ana musayar wuta, sojojin tsaron kasar sun kwantar da kurar farmakin da aka kaiwa otal din Intercontinental dake Kabul, babban birnin kasar.

A cikin sanarwar da ma'aikatar ta fitar, an ce mahara su 4 sanye da rigar dake makale da boma-bomai, sun kutsa cikin hotel din da karfe 9 na daren ranar 20 ga wata suka kuma bude wuta, nan take kuma aka fara bata kashi tsakanin su da sojojin tsaron kasar. A karshe dai sojojin tsaro sun ceto mazauna hotel din 160, ciki har da 'yan kasashen ketare 41.

A daren ranar 21 ga wata, ministan harkokin wajen kasar Ukraine Pavlo Klimkin ya tabbatar da cewa, jama'ar kasar sa 6 ne sun rasa rayukansu sakamakon farmakin da aka kai a hotel din na Intercontinental dake birnin Kabul. (Bilkisu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China