in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
'Yan ci ranin Afirka 15 sun mutu a gabar ruwan Aljeriya
2018-04-30 16:04:22 cri
Rahotanni daga kasar Aljeriya na cewa, kimanin 'yan ci-ranin Afirka 15 dake kokarin shiga kasar ba bisa ka'ida ba ne suka mutu, bayan da kwale-kwalen da suke ciki ya nutse a gabar ruwan gabashin kasar.

Kamfanin dillancin labaran kasar ya ce, masu tsaron gabar teku sun yi nasarar ceto wasu mutane 19 cikin 34, dukkan su daga kasashen Afirka, lokacin da kwale-kwalen da suke ciki ya nutse a gabar ruwan Cape Falcon dake lardin Oran, kimanin kilomita 400 daga yammacin birnin Algiers.

Ana tunanin rashin kyan yanayi ne ya haddasa hadarin. Har yanzu dai masu tsaron tekun na neman ragowar gawawwakin mutanen da suka mutu.

A cewar tashar talabijin na Ennahar, kwale-kwalen ya taso ne daga Morocco a kan hanyarsa ta zuwa Turai, amma sai iska mai karfi ta canza akalarsa zuwa gabar ruwan Aljeriya.

Kasar Aljeriya dai ta kasance hanyar da bakin hauren Afirka ke amfani da ita wajen shiga Turai. Ministan harkokin cikin gidan Aljeriya Noureddine Bedoui ya bayyana a kwanakin nan cewa, a kullum sojojin da aka girke a iyakar kudancin kasar suna dakile yunkurin bakin haure daga kasashen Afirka dake yankin Sahara sau 500 na shiga kasar ba bisa ka'ida ba.

Bayanai na nuna cewa, a cikin shekaru ukun da suka gabata mahukuntan kasar sun tusa keyar bakin haure kimannin 27,000 zuwa kasashensu, lamarin da ya gamu da wasu kungiyoyin masu zaman kansu sokar gwamnati da gallazawa bakin hauren. (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China