in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
CISSA ya sanar da shirinsa na magance matsalar bakin haure
2018-02-27 10:36:57 cri

Kwamitin leken asiri da kula da harkokin tsaro a nahiyar Afrika CISSA, ya sanar da wani shirin hadin gwiwa da ya yi da tarayyar kasashen Afrika AU da MDD na datse hanyoyin safarar bil adama da kwararar bakin haure.

A jiya Litinin ne aka kaddamar da taron tuntuba na kwamitin a birnin Khartoum na kasar Sudan, inda ya samu halartar hukumomin leken asiri 17 daga kasashen Afrika da jami'ai daga hukumar kula da ayyukan AU, domin tattauna laifukan kaura ba bisa ka'ida ba da kuma safarar bil adama.

Cikin jawabinsa na bude taron, sakataren zartaswa na kwamitin Shimelis Woldesemayat, ya ce safarar bil adama ta zama laifi mafi girma na biyu a duniya.

Ya ce, shirin kwamitin, ya dogara ne kan hadin gwiwar AU da MDD da tarayyar Turai, a wani muhimmin mataki na aiki game da yadda za a tunkari matsalolin safarar bil adama da kwararar bakin haure. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China