in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin tana fatan bangarori daban daban za su ci gaba da martaba yarjejeniyar nukiliyar Iran
2017-10-10 20:18:27 cri
Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Hua Chunying ta bayyana a gun taron manema labaru da aka gudanar a yau Talata a nan birnin Beijing cewa, Sin tana fatan bangarori daban daban za su ci gaba da martaba yarjejeniyar nukiliyar kasar Iran.

A kwanakin baya ne, babban direktan hukumar makamashin nukiliya ta duniya wato IAEA ya bayyana cewa, kasar Iran ta sauke nauyin da ke kanta na martaba yarjejeniyar nukiliyar kasar da aka cimma. Kungiyar EU, da kasashen Rasha, Jamus da sauran kasashe sun yaba da yarjejeniyar nukuliyar kasar Iran din da aka cimma. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China