Sandar alama ce ta girma ga zaurukan majalisun dattawa da na wakilan kasar.
Wadanda suka yi tsokaci kan al'amarin, sun bayyana shi a matsayin abun kunya ga Nijeriya, wadda ta fi kowacce kasa yawan al'umma a nahiyar Afrika.
'Yan sanda dai sun ce sun gano sandar da wasu da ba a san ko su waye ba suka sace daga zauren majalisar dattawa.
Ana zargin wasu bata gari da kutsawa zauren majalisar yayin da ta ke zamanta a ranar Laraba, inda suka yi awon gaba da sandar.
Mai Magana da yawun 'yan sanda a kasar Aremu Adeniran, ya ce an jefar da sandar ne a karkashin wata gadar sama, dake kusa da kofar shiga cikin birnin Abuja. Wani dake wucewa ne ya gani tare da shaidawa 'yan sandan.
Cikin wata sanarwa da ya fitar, kakakin majalisar Sabi Abdullahi, ya zargi 'dan majalsiar da aka dakatar Ovie Omo-Agege da jagorantar matasan da suka sace sandar yayin zaman majalisar.
Abdullahi Sabi ya bayyana al'amarin a matsayin babban laifin bijerewa kasa, wanda zai haifar da karbe ragamar majalisar dattawan.
A nasa bangaren, mataimakin shugaban majalsiar wakilan kasar Yusuf Lasun, ya bayyana dauke sanadar a matsayin abun da ya kunyata demokradiyyar kasar, yana mai cewa, zauren majalisar na 8 zai tabbatar da demokradiyya ta yi aiki a kasar. (Fa'iza Mustapha)